ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a cikin watan Afrilun da ya gabata ne aka kammala cinikin, sannan jami’an gwamnatin kasar ta Masar zasu kammala sanya hannu a kan wannan cininin a birnin Paris a yau Talata.
Kafin haka dai shugaba Emmanuel Maocron yak i amincewa da sayarwa kasar Masar jiragen yakin don abinda ya kira ayyukan take hakkin bil’adama a kasar.
Banda haka ana saran faransa zata sayarwa kasar ta Masar makamai masu linzami samfurin Safran da dama wadanda kimarsu ya kai uro miliyon 200.
342/