4 Mayu 2021 - 14:20
Borrell : Ya Kamata A Yi Amfani Da Damar Da Ake Da Ita, Domin Amurka Ta Koma A Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Babban jami'in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai ya jaddada wajabcin amfani da damar diflomasiyyar da ake da ita don sanya Amurka komawa ga yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015 da kuma share fagen aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar.

ABNA24 : A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, Josep Borrell ya ce ya tabo batun yarjejeniyar Iran, yayin taron ministocin harkokin waje na kungiyar G7 ta kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya dake gudana a birnin Landan.

Furicin na Josep Borrell, na zuwa ne bayan da aka dakatar da tattaunawar da ake a Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar ta Iran.

Batun sake komawar Amurka a cikin yarjejeniyar da km adage wa Iran takunkumi su ne manyan batutuwan da suka mamaye tattaunawar.

A ranar Juma’a mai zuwa ce wakilan bangarorin da yarjejeniyar ta shafa zasu koma tattaunawar ta Vienna.

342/