ABNA24 : Majiyar ta kara da cewa an yi wata ganawar sirri a tsakanin jami’an Iran da na Birtaniya akan batun, da zai bude kafar dawo wa da Iran din kudadenta.
A gefe daya wata majiyar ta ce Iran za ta saki Nazanin Zaghari wacce aka kama da yi wa Birtaniya leken asiri da hakan ya sa aka yanke ma ta hukuncin zaman kurkuku na shekara guda.
Jami’an leken asirin Iran sun kame matar ne a filin saukar jiragen sama na Imam Khumaini a lokacin da take kokarin tafiya London da take zaune a can a ranar 3 ga watan Aprilu na 2016.
342/