ABNA24 : Shugaban cibiyar da ke kula da samar da rigakafin cutar ta COVID-19 Hojjat Nikki-Maleki ne ya sanar da hakan, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce sakamakon aiki tuƙuru na masana da ƙwararrun Iran a halin yanzu an fara samar da rigakafin na COVIran Barekat tun ma kafin lokacin da aka tsara za a yi din wanda shi ne a tsakiyar watan Mayu mai kamawa.
Jami’in ya bayyana cewar cikin makonni uku masu zuwa za a samar da alal aƙalla allurar rigakafin da za ta kai miliyan guda, kamar yadda kuma ya ce daga baya kuma cikin watanni masu kamawa za a samar da rigakafin da suka kai miliyan uku lokacin da za a fara yin rigakafin cutar ta gama gari a duk faɗin ƙasar.
A wata sabuwa kuma Iran ɗin ta soma shiri na uku na gwajin rigakafin cutar ta Korona inda aka gwada rigakafin kan wasu mutane.
Iran dai tana ƙoƙarin samar da rigakafin cutar Koronan ne a cikin gida don amfanin al’ummarta musamman sakamakon irin takunkumin da Amurka ta sanya mata da ke hana ta shigo da kayayyaki daga waje ciki kuwa har da magunguna.
342/