ABNA24 : Ofishin jin kai na MDD (OCHA) ya ce, yanayin bukatar jin kai na dada tsananta a shiyyar, inda aka yi kiyasin kusan mutane miliyan 29 za su bukaci tallafi a bana, adadin da ya karu da mutum miliyan 5 bisa na shekarar 2020 data gabata.
Rahoton na OCHA ya ce, daga shekarar 2015 zuwa 2020, hare haren da aka kaddamar ya ninka har sau takwas a tsakiyar yankin Sahel, kana ya ninka sau uku a yankin tafkin Chadi.
A cewar OCHA, a yankin tafkin Chadi kadai, mutane miliyan 6.2 suna fuskantar matsalar yunwa a shekarar nan, inda aka samu karin kusan mutane miliyan biyu sama da na bara.
A yankin tsakiyar Sahel wanda ya kunshi kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, mutane miliyan 3.4 na fuskantar matsalar abinci a cikin wannan shekara ta 2021, wanda ya kai matakin koli.
Hukumar tana neman dala biliyan 3.7 domin shirya ayyukan tallafin jin kai a kasashen Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Mali, Nijar da Najeriya.
342/