28 Afirilu 2021 - 13:19
​Shugaban Somalia Ya Sanar Da Aniyarsa Ta Mika Mulki

Shugaban kasar Somalia Muhammad Abdullah Muhammad ya sanar da aniyarsa ta mika mulki tare da janye batun yin tazarce a kan shugabancin kasar.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya Shugaban kasar Somalia Muhammad Abdullah Muhammad ya bayyana cewa, zai mika mulkin kasar ba tare da wani bata lokaci ba, da zaran an gudanar da zabuka.

Ya cea halin yanzu abin da ke da muhimmanci shi ne shirya zabuka, kuma zai bayar da himma kan hakan, kuma yana yaba wa dukkanin wadanda suka nuna mahangarsu ta kishin kasa kan hakan.

Shugaban na Somalia dai ya fuskanci matsin lamba daga ciki da wajen kasar, bayan da yaki yarda a gudanar da zabuka, tare da kara wa kansa wa’adin mulki na tsawon shekaru biyu a nan gaba, lamarin da ya jawo tashe-tashen hankula a birnin Mugadishu a cikin wannan mako.

Yanzu haka wasu daga cikin manyan jami’an tsaro na soji da ‘yan sanda na kasar ta Somalia sun fara juya masa baya kan wannan mataki da ya dauka, kamar yadda shi ma Firayi ministan kasar ta Somalia ya nuna adawarsa a fili kan matakin na shugaban kasa, lamarin da ake ganin shi ne ya tilasta shi dawowa daga rakiyar mafarkin yin ta zarce a kan mulkin kasar.

342/