27 Afirilu 2021 - 12:35
Fiye Da Mutane 800,000 Aka Yi Wa Allurar Rigakafin Corona A Iran

A wata sanarwa da ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ta yi, ta bayyana cewa; Mutanen da aka yi wa bangaren farko na allurar rigakafin corona sun kai 171, da 210, sai kuma wadanda aka yi wa na farko da na biyu da su ka kai 652 da 903.

ABNA24 : Jumillar wadanda su ka samu aka yi musu allurar sun kai dubu dari takwas da ashirin da hudu da dari daya da goma sha uku.

A gefe daya, mutanen da cutar ta corona ta kashe a cikin san’oi 24 da suka gabata a Iran sun kai 496, sai kuma wadanda su ka kamu da ita da suka kai 21,026.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ta sanar da cewa; Daga bullar cutar corona zuwa yanzu adadin wdanda su ka mutu a Iran sun kai 70,070.

342/