20 Afirilu 2021 - 14:51
Shugaba Idriss Deby Itno Na Chadi Ya Rasu, Bayan Samun Rauni

Rundinar sojin kasar Chadi, ta sanar da mutuwar shugaban kasar Idriss Deby Itno, sakamakon rauni da ya samu a fagen daga na jare martabar kasar.

ABNA24 : Idriss Deby, ya samu rauni ne jiya, kuma ya rasu a asibiti sakamakon raunin da ya samu a goshi lokacin fada da 'yan tawayen kasar.

Dan shekara 68 Marshal Idriss Deby, ya kwashe shekara 30 yana mulkin wannan kasa ta Chadi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar zaben kasar mai zaman kanta (CENI) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar a karo na shida.

Tuni dai aka kafa majalisar sojoji da zata shugabanci kasar wacce dan mirigayin Janar Mahamat Deby Itno, zai jagoranta na tsawon watanni 18.

A halin da ake ciki dai an kafa dokar ta baci a duk fadin kasar, tare kuma da rufe dukkan iyakokin kasar.

342/