18 Afirilu 2021 - 13:59
Imam Khamenei Ya Buƙaci Sojojin Iran Da Su Кara Zama Cikin Shirin Da Ake Buƙata

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya buƙaci sojojin ƙasar Iran da su ƙara zama cikin shiri da kuma ƙarfafa irin ƙarfin da suke da shi gwargwadon irin buƙatar da ake da ita.

ABNA24 : Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya aike wa babban hafsan hafsoshin ƙasa na ƙasar Iran, Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, gabanni zagayowar Ranar Sojoji ta Кasar Iran.

A cikin saƙon Imam Khamenei ya bayyana cewar: Ka isar da gaisuwa tag a jami’an soji da iyalansu masu girma., A yau sojoji suna nan a dukkanin fagage kuma a shirye suke su gudanar da ayyukansu. Don haka ku ƙara irin wannan shirin da kuke da shi gwargwadon buƙata sannan kuma su sauƙe nauyin da ke wuyanku.

An shigar da Ranar Sojoji ta Кasa cikin kalandar ƙasar Iran ne bayan wasiƙar da marigayi Imam Khumaini, wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekara ta 1979 inda ya nuna goyon bayansa ga sojojin da kuma umurtarsu da su gudanar da fareti na gama gari a duk faɗin ƙasar a ranar 18 ga watan Aprilu na kowace shekara.

342/