ABNA24 : Anton Khlopkov wanda jaridar Kamresanet ta kasar Rasha ta yi hira da shi ya kara da cewa; Matakin na Iran zai iya sanya Amurka ta daina jan kafar da take yi, domin daukar matakan siyasar da za su kai ga cimma yarjejeniya.
A jiya Asabar ne dai aka bude tattaunawar kwamitin hadin gwiwa na yarjejeniyar Nukiliya a birnin Vienna wanda ya sami halartar Iran da saukar kasashen suke cikin yarjejeniyar. A yayin tattaunawar ta jiya an yi bitar sakamakon tarukan da aka yi a baya, da kuma batun dauke wa Iran din takunkuman da aka kakaba mata.
342/