ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Sa’id Namaki ministan kiwon lafiya na kasar ya na fadar haka, ya kuma kara da cewa za’a gaggauta samar da alluran na cikin gida ne don fuskantar annobar ta korona musamman a cikin mummunan halin da cutar da jefa kasar a halin yanzu.
Banda haka ofishin jakadancin kasar Iran a birnin Mocso ya bada sanarwan cewa an kammala cinikin karin alluran riga kafin cutar har miliyon 60 daga kasar ta Rasha, samfurin Sputnik V don ganin an shawo kan yadunar cutar a cikin kasar.
Ministan kiwon lafiya na kasar ya kammala da cewa ya zuwa yanzu an yiwa mutani kumani dubu 500 a alluran riga kafin, kuma ana saran nan da mako guda adadin zai kai 1,300,000.
Ya zuwa yanzu dai Iran ta shigar da alluran riga kafin cutar ta korona daga kasashen Rasha, China da kuma Korea ta Kudu.
342/