ABNA24 : Jalal Fayruz wanda kamfanin dillancin labarun ( Irna) ya yi hira da shi da safiyar yau Asabar, ya ci gaba da cewa; Shekaru 10 sun shude daga fara yunkurin kawo sauyi a kasar Bahrain, amma har yanzu yanayin kasar yana cikin muni.”
Tsohon dan majalisar kasar ta Bahrain ya kuma bayyana cewa; har yanzu mahukuntan kasar suna ci gaba kai wa mutane hari a gidajensu tare da kama su.
Bugu da kari Feyruz ya ce; Har yanzu ana ci gaba da kama masu wallafa ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta.
342/