13 Afirilu 2021 - 12:54
​Ramadan: Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Yi Hasashen Kara Yaduwar Cutar Korona A Cikin Watan

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi hasashen cewa mai yuwa cutar Korona ta kara yaduwa a cikin watan ramalan mai kamawa, saboda haduwar musulmi a cikin watan zai kara yawa saboda dalilai da dama.

ABNA24 : Jaridar Tribune ta Najeriya ta nakalto hukumar ta na gargadin musulmi masu azumi da su yi hattara a cikin watan don kada cutar ta kara yaduwa.

A halin yanzu ana cikin kulle a kasashen musulmi da dama, mai yuwa idan watan ta ya shigo haduwar musulmi musamman cikin dare zai kara yawa, wanda kuma zai bada dama ta yaduwar cutar.

Kasashen Saudia, Yemen, Masar da kuma Tunisia sun bada sanarwan cewa yau litinin ce ranar karshe na watan shaaban don haka gobe Talata ce farkon watan ramala.

342/