ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce a halin da ake ciki dai ana ci gaba da kidayen kuri’un a aka kaɗa a mazaɓu daban-daban kuma ana sa ran a nan gaba za a sanar da sakamakon zaɓen, wanda a bisa doka dai hukumar zaɓen ƙasar tana da har zuwa ranar 25 ga watan Aprilun nan na ta sanar da sakamakonsa.
Shugaba Deby ɗin dai wanda ya kaɗa kuri’arsa tun da sanyin safiyar Lahadin yayi watsi da zargin danne ‘yan adawa da kuma kiran da wasu suke yi na a ƙaurace wa zaɓen, yana mai fatan lashe zaɓen da zai ba shi damar ci gaba da shugaban Chadin a wa’adi na shida.
A ƙasar Benin ma dai da aka gudanar da zaɓen a jiya, al’umma na ci gaba da jiran sakamakon zaɓen inda a nan ma ake ganin shugaban ƙasar mai ci ga Patrice Talon ne zai lashe zaɓen musamman bisa la’akari da ƙaurace wa zaɓen da ‘yan adawa suka yi.
Shugaba Patrice Talon mai neman wa’adi na biyu, ya fafata ne da manyan masu hamayya da shi guda biyu a zaben wato Alassane Soumanou da Corentin Kohoue.
Saidai yawancin shugabannin ‘yan adawa sun fice daga kasar bayan da kotu ta haramta masu shiga zaben.
342/