10 Afirilu 2021 - 01:00
Nijar : An Sake Fitar Da Hama Amadu Waje Domin Neman Magani

Bayanai daga Jmahuriyar Nijar na cewa an sake fitar da tsohon madugun ‘yan adawa na kasar Malam Amadou zuwa kasar Faransa domin neman magani.

ABNA24 : Rahotanni da kusoshin jam’iyyarsa ta Moden Lumana, suka tabbatar sun ce an fitar da Hama Amadou ne a cikin daren ranar Laraba zuwa Faransa inda zai je zuwa asibiti domin neman magani.

Babu wani babban abun damuwa game da yanayin kiwon lafiyarsa a cewar makusantansa.

Ana dai tsare da Hama Amadou ne a gidan kason Filingue, kwanaki biyu bayan tarzomar data barke bayan sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, da dan takarar jam’iyya mai mulki Malam Bazoum Mohamed ya lashe.

Wannan ba shi ne karon farko ba da Hama Amadou ke zuwa neman magani a Faransa, a lokacin da ake tsare da shi a gidan yari, don kuwa ko a 2016 Hama ya bar gidan yarin na Filingue bisa dalilai na rishin lafiya.

Ya koma NIjar ne a watan Nuwamba na 2019 lokacin rasuwar mahaifiyarsa, daga bisani kuma ya mika kansa ga kotu, wace ta tisa keyarsa a gidan yari, amma daga baya aka sallame shi.

342/