ABNA24 : Kasar Habasha ta na tsammanin samun ci gaban tattalin arziki mai yuwa da kuma wutan lantarki mai yawa saboda madatsar ruwan, amma gwamnatocin kasashen Masar ta Sudan sun ce ba za su amince da dukkan wani abu da zai rage yawan ruwan da ke kwarara zuwa kasashensu daga kogin Nilu ba.
Tawagar kasashen uku sun hadu a birnin Kinsasha na kasar Democdiyyar Congo don tattauna matsalolinsu dangane da madatsar ruwan, amma har aka tashi basu cimma wata matsaya dangane da matsalarba.
Kasashen Masar da Sudan dai sun bukaci a samar da wani tsari wanda gwamnatin kasar Habasha za ta yi amfani da shi waje sarrafa ruwan madatsar, ta yadda hakan ba zai rage yawan ruwan da ke kwara zuwa kasashensu ba, Amma gwamnatin kasar Habasha ta ki amincewa da haka. Don ta na ganin ruwan na ta ne kuma wani ba zai tsara mata yadda zata yi amfani da su ba.
342/