6 Afirilu 2021 - 13:13
Tsohon Yarima Mai Jiran Gadon Jordan Ya Ce Ba Zai Bi Umurnin Sojojin Кasar Na Yayi Shiru Ba

Tsohon yarima mai jiran gado na ƙasar Jordan wanda kuma a halin yanzu aka masa ɗaurin talala, Yarima Hamza, ya ce ba zai bi umurnin sojojin ƙasar na rufe bakinsa da kuma daina tattaunawa da wasu mutane na daban ba.

ABNA24 : Yarima Hamza, wanda kuma ƙani yake wa sarki Abdullah na biyu na ƙasar Jordan, ya bayyana hakan ne cikin wani sautin da ya aika wa wata kafa a yau ɗin nan Litinin sannan kuma ‘yan adawar ƙasar suka watsa inda ya ke cewa ba yana so ne ya sake dagula lamurra ba, to sai dai ya ce ko shakka babu ba zai bi umurnin hana shi magana da mutane ko kuma rubutu a shafinsa na Twitter ba ko kuma hana shi ganawa da iyalinsa ba.

A jiya Lahadi ne mataimakin firayi ministan ƙasar Jordan ɗin ya sanar da cewa Yarima Hamzah, ɗan shekaru 41 ya kasance yana haɗa baki da wasu ‘yan ƙasashen waje wajen ƙulla makircin ruguza ƙasar.

Kafin nan sojojin ƙasar sun sanar da cewa tuni sun ja kunnen Yarima kan wasu ayyuka da yake yi da ke barazana ga tsaron ƙasar, lamarin da daga baya Yariman ya ce mahukutan ƙasar sun yi masa ɗaurin talala.

Yarima Hamzah ya kasance Yarima mai jiran gadon ƙasar ta Jordan tun daga shekarar 1999 lokacin da tsohon sarkin Jordan ɗin kuma mahaifinsu Sarki Husein ya rasu, to sai dai daga baya a shekara ta 2004, sarkin Jordan ɗin na yanzu Sarki Abdullah na biyu ya tuɓe shi daga wannan muƙamin.

342/