ABNA24 : Jaridar Leadership ta Hausa ta nakalto shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu , shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a taron da ya yi da su a hedikwatar hukumar a Abuja a ranar Alhamis.
Mahmood ya ce, ‘bayan mun duba wadannan matsaloli da matakan da muka dauka don magance su, a yanzun hukumar ta kai matsayin da za ta iya bayyana ranar Litinin 28 ga watan Yuni na shekara ta 2021 a matsayin ranar da za mu koma mu ci gaba da rijistar katin zabe(CVR) a duk fadin kasar.’
Farfesa Mahmood ya kara da cewa za’a ci gaba da wannan rijistar har zuwa karshen shekara ta 2022, wato watanni kadan kafin a gudanar da zabubbuka a kasar.
Daga karshen shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ya kammala da cewa, an dakatar da rijistar mutane ne saboda cutar korona da ta bulla a kasar a farkon shekarar da ta gabata.
342/