ABNA24 : Kamfanin dillancin labarun “ Patra’ na kasar Jordan ya amabci sunan Sharif Hassan Bin Zaid da Ibrahim Awadallah daga cikin wadanda aka kama.
Ita kuwa jaridar “Washington Post” ta bayar da labarin dake cewa; Daga cikin wadanda ake tsare da su a gida da akwai tsohon Yarima mai jiran gado, Hamza Bin Husain, sai dai majiyar gwamnatin kasar ta kore hakan.
Jaridar ta ci gaba da cewa; kame mutanen da aka yi a kasar yana a karkashin wata makarkashiya ce ta kwace mulki daga hannun sarki Abdullah Bin Husain.
Wasu daga cikin wadanda aka kama sun hada jami’an tsaro da shugabannin haulolin Larabawa.
342/