ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, an ji karar tashin boma-boman hatta a yankunan da suke kusa da unguwar don karfinsu.
Amma har ya zuwa lokacin bada wannan labarin ba’a san irin asarori na rayuka da dukiyoyin da fashefashen suka haddasa ba.
A cikin watannin biyu da suka gabata dai an yi ta kai hare-haren ta’addanci a birnin na Bagadaza. Sannan an kai harin na jiya jumma’a ne a dai-dai lokacinda shuwagabannin kasashen Masar, Jordan da kuma kasar ta Iraki suke taro a birnin.
342/