4 Afirilu 2021 - 06:16
Hukumar Kare Haƙƙoƙin Bil’adama Ta Nijar Ta Buƙaci Gudanar Da Bincike Kan Zargin Fyade Da Ake Wa Sojojin Chadi

Hukumar kare haƙƙoƙin bil’adama ta ƙasar Nijar ta buƙaci gudanar da bincike mai cin gashin kansa kan zargin fyaɗe da ke yi wa sojojin ƙasar Chadi da aka tura su Nijar ɗin don faɗa da ƙungiyoyin ta’addanci, ciki kuwa har da fyaɗen da aka yi wa wata yarinya ‘yar shekaru 11.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce hakan yana cikin wani rahoto ne da hukumar ta fitar bayan gudanar da wani bincike da kuma shaidun da ta samu da kuma binciken likitanci da aka gudanar kan waɗanda ake zargin an musu fyaɗen ciki kuwa har da wasu mata guda biyu.

Rahoton ya ce matan biyu, wadda ɗaya daga cikinsu tana da ciki, an musu fyaɗen ne a gaban mazajensu waɗanda sojojin suka kama da kuma tsare su.

Rahoton ya ƙara da cewa akwai wasu matan da aka yi musu fyaɗen ko kuma ƙoƙarin yi waɗanda suke tsoron su fito su faɗi saboda tsoro.

Baya ga batun fyaɗen har ila yau kuma ana zargin sojojin Chadin, inji rahoton, da ƙwace kayayyakin mutane a yankin Tera da ke kan iyaka da ƙasar Burkina Faso inda aka tura sojojin.

Har yanzu dai gwamnatocin ƙasashen biyu, wato Nijar Da Chadi ba su ce komai kan wannan lamari ba.

342/