ABNA24 : Wannan harin ya yi sanadiyyar kashe fararen hula masu yawan gaske da su ka hada ‘ yan kasar da kuma bakin haure.
Sanarwar da kungiyar ta ‘yan ta’adda mai son kafa abinda take kira; Halifanci Na Musulunci” wacce ta watsa a shafin “Twitter ta kunshi cewa; “ Sojojin Halifanci sun kwace iko da garin Palma mai muhimmanci”
Jirgin ruwa na Sea Star, ya isa Pemba a ranar Lahadi dauke da mutane 1,400, mafi yawancinsu ma’aikatan kamfanin Total.
Wani jirgin ruwan ma ya isa garin na Pemba dauke da mutane a ranar Lahadi da tsakar rana shi ma dauke da mutane.
342/