ABNA24 : Husain Ashtari ya kuma kara da cewa; Bisa hasashen da su ka yi babu wata matsala mai alaka da tsaro da za a fuskanta a lokacin zabukan.
Har iya yau, kwamandan ‘yan sandan na Iran ya tabo shirin da su ka yi domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan shigar sabuwar shekara na Nowruz, wanda kuma har yanzu yana ci gaba.
Nan da watanni biyu masu zuwa ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasar karo na 13, da kuma zaben ‘yan majalisar karo 60, sai kuma zabukan kananan hukumomi.
Wasu daga cikin zabukan da za a yi a lokacin sun hada da na Majalisar kwararru masu zabar jagoran juyi da sanya idanu akan ayyukansa.
342/