22 Maris 2021 - 08:18
Imam Khamenei:Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Iran Laifi Ne Babba Kuma Ya Sabawa Diblomasiyya

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyed Aliyul Khamenei ya bayyana cewa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta daurawa kasar wani laifi ne babba da ta aikata, wanda ya kamata duniya ta sani.

ABNA24 : Imam Khamenei ya bayyana haka ne a yau Lahadi a lokacinda yake jawabi na shigowar sabuwar shekara ta Iraniyawa wato hijira shamsiyya wacce take cika shekaru 1400 a yau.

Jagoran ya kara da cewa takunkuman tattalin arzikin da wasu manya-manyann kasashen duniya suka durawa wasu kasashen a duniya babban laifin ne wanda ya sabawa tsarin damocrdiyya da kuma diblomasiyya a duniya.

Kafin haka jagoran ya sanya sabuwar shekara ta Iraniyawa, shekara samar da kayaki a cikin gida tallafawa masana’antu da harkokin kasuwanci da kuma dauke matsalolin da suke hana kasar ci gaba.

A cikin jawabinsa jagoran ya bayyana cewa muaten kasar Iran sun maida bazaranar takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar zuwa dama, don sanadiyyar watakunkuman kasar ta wadatu daga kasashen waje a fannoni da dama, kamar da takunkuman rufe baki a zamanin cutar korona har zuwa manzya manya kamfanoinin kereker, musamman kamfanonin kera kayakin cikin gida.

A wane bangaren na jawabinsa jagoran ya bayyana cewa gwanatocin Amurka ta yanzu da kuma wadanda suke shude sun yi kura kurai da dama, dangane da yarjejeniyar PCPOA, mamayar kasar Siriya, dangane da Palasdinu da kuma kasar Yamen. Kuma har yanzun tana kan wadannan kura-kuran.

Matsin lambar na Amurka, ya kara wa Iran karfi da kuma sanya ta kara zama mai dogaro da kanta, inji jagoran, sannan ya sake nanata cewa Iran, na nan kan bakarta na cewa sai Amurka ta dage mata dukkan takunkuman data kakaba mata, kafin Iran ta dakatar da matakan da take dauka na dakatar da aiki da wasu bangarori da yarjejeniyar nukiliyar 2015 ta kunsa, inji shi.

Idan Amurka ta dage takunkumai, kuma muka ga hakan a zahiri, to zamu dakatar da matakan da muka dauka.

Imam Khamenei, ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya gabatar, na shiga sabuwar shekarar ta kalandar Iraniyawa ta hijira shamsiyya 1400, da aka shiga a jiya Lahadi.

342/