ABNA24 : A sakamakon dindindin data fitar da yammacin jiya Lahadi, kotun ta ce Bazoum Mohamed, ya lashe zaben da kashi 55,66 cikin dari na jimmilar kuri’un da aka kada, yayin da dan takaran adawa tsohon shugaba Alhaji Mahamane Usman karkashin jam’iyyar RDR-Tchanji, ya samu kashi 44,34 cikin dari.
Sakamakon dai ba shi da wani bambanci na azo a gani, idan aka kwantanta shi da na wucin gadi da hukumar zaben kasar ta CENI, ta fitar a ranar 23 ga watan Fabarairu, duk da korafen korafen da jam’iyyun adawa na kasar suka gabatar game da wasu kura kurai da suka ce an tafka a zaben.
Kotun ta kuma ayyana Bazoum Mohamed, a matsayin zababen shugaban kasar, wanda wa’adin mulkinsa na farko zai fara aiki daga ranar 2 ga watan Afrilu mai zuwa, inda zai maye gurbin shugaba mai barin gado Mahammadu Issoufou dake kan kammala wa’adin mulkinsa na biyu kuma na karshe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
342/