20 Maris 2021 - 16:40
Najeriya:’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 13 Sannan Sun Raunata Wasu 7 A Jihar Kaduna

Kwamishinan watsa labarai na gwamnatin jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bada sanarwan cewa ‘yan binda sun kashe mutane 13, sannan sun raunata wasu 7 a kananan hukumumi Zangon Kataf, Kaura da kuma Chikun na jihar.

ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Aruwan yana fadar haka a jiya jumma’a ya kuma kara da cewa, da farko ‘yan bindigan sun kashe wani mutum wanda ake kira Irmiya Godwin a lokacinda shi da dan’uwanda suke dawowa daga gona a kauyen Gora Gan a karamar hukumar Zangon Kataf, amma dan’uwansa ya tsira daga harin, sannan sun kashe mutane 10 a garin Kizashi na karamar hukumar Kaura banda haka sun kona gidaje 56 da babura 16. Kwamishin ya kammala da cewa wadanda aka kashe sune

Esther

Bulus, Maria Bulus (dan shekara guda diyar Esther), Lami Bulus, Aliyu Bulus,

Monday Joseph, Geje Abuba, Wakili Filibus, Yakubu Ali., Dije aziri, Joseph

Ibrahim .

Sannan wadanda suka ji rauni kuma sun hada da : Cecilia Aku, Yakubu Idi, Godiya Saleh da kuma Moses Adamu.

342/