20 Maris 2021 - 16:38
Kasar Niger, Za Ta Bunkasa Tsaro Bayan Wani Mummunan Hari Da “Yan Ta’adda Su Ka Kai A Ranar Litinin

Ministan harkokin cikin gida Alkache Alhada ya bayyana cewa; harin da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 66.

ABNA24 : Babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin,sai dai kasar tana fuskantar kalubale mai grima na tsaro daga kungiyoyin bokoharam da ISWAP.

Ministan ya kara da cewa; Za mu kara yawan jami’an tsaro da za su rika yin sintiri daga kauye zuwa kauye, sannan kuma da tabbatar da cewa an samarwa da jami’an tsaron kayan abincin da suke bukata da shi.”

A ranar juma’ar da ta gabata ne, gwamantin kasar ta Nijar ta kira yi al’ummar kasar da su zama masu sanya idanu akan harkokin tsaro, tare da jaddada aniyarta ta fada da ayyukan laifi.

342/