17 Maris 2021 - 13:04
Manyan Kasashen Turai, Sun Dakatar Da Amfani Da Rigakafin AstraZeneca

Wasu kasashen turai guda hudu, da suka hada da Faransa, Jamus, Italiya da kuma Spain, sun sanar a jiya Litini da bin sahun kasashen da suka dakatar da amfani da riga kafin cutar korona na kamfanin AstraZeneca.

ABNA24 : Kasashen sun sanar cewa sun dau wannan matakin ne saboda dalilai na kiyayewa, biyo bayan bayyanan cewa ana samun daskarewar jini ga mutanen da akayi wa riga kafin na AstraZeneca.

Kuma kasashen sun ce suna kan jiran rahoton da hukumar magunguna ta turai da ake sa ran za’a fitar yau Talata.

Saidai kamfanin harhada magungunan na hadin guiwar Ingila da Sweden, ya ce kawo yanzu babu wata hujja mai hadari, ta daskarewar jini da riga kafin kan haifarwa.

To saidai Yayin da manyan kasashen suka dakatar da amfani da rigakafin na AstraZeneca saboda rahotannin illar da aka ce yanayi, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce bata ga wata illah da maganin yake da shi ba kawo yanzu.

342/