ABNA24 : Kakakin gwamnatin Nijar ɗin Abdourahmane Zakaria ne ya sanar da hakan ta gidan talabijin ɗin ƙasar a yammacin jiya inda ya ce kisan gillan da aka yi wa mutanen ya faru ne ranar Litinin a yankin na Tillabery da ke kan iyakan Nijar ɗin da ƙasashen Mali da Burkina Faso.
Kakakin gwamnatin ya gwamnatin ta sanar da juyayi na kwanaki uku a matsayin kwanakin makoki na ƙasa don tunawa da waɗanda suka rasa rayukan na su.
Har ya zuwa yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗau alhakin kai wannan harin sai dai kuma da dama suna ganin irin waɗannan hare-hare ba za su rasa alaƙa da ƙungiyoyi masu tsaurin ra’ayin addini masu alaƙa da ƙungiyoyin Al-Кa’ida da ISIS da suke gudanar da ayyukansu a yankin ba.
Wannan harin dai yana nuni da irin gagarumin ƙalubale na tsaro da ke gaban sabon shugaban Nijar ɗin Mohamed Bazoum wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a watan Fabrairun nan da ya gabata don ya gaji shugaba mai barin gado Mahamadou Isoufu.
342/