15 Maris 2021 - 14:57
Somaliya Da Kenya Sun Fara Shari'a Kan Rikicin Iyakar Teku

A wani lokaci yau Litinin ne ake sa ran kotun kasa da kasa ta MDD, za ta soma zaman shari'a kan takkadamar dake tsakanin kasashen Kenya da Somaliya game da kan iyakar teku dake tsakaninsu.

ABNA24 : Saidai tun kafin a kai ko ina, Kenya ta zargi kotun da nuna son rai, don haka ta yanke shawarar cewa ba za ta halarci zaman shari’ar ba.

Kenya, ta kuma nuna rashin amincewa da kasancewar wani alkali dan Somaliya a rukunin alkalan da za su yi shari'ar.

Takaddamar kan yankin mai dumbin arzikin mai da iskar gas ta haifar da ricikin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

A shekara ta 2014 ne dai Somaliya ta shigar da kara game da yankin da take takaddama a kai da kasar Kenya.

Ta ce kamata ya yi fasalin iyakar ruwa ya yi daidai da fasalin iyakar kan tudu, yayin da ita kuma Kenya ta ce a ko yaushe a kan dauki tsarin iyakar ne a mike, daga inda kasashen biyu suka hade a gabar ruwan.

342/