ABNA24 : Babu wani karin haske daga gamayar kungiyoyin kan daukar matakin, amma sun ce nan gaba zasuyi bayyani game da gwagwarmayar da suke, ciki harda bukatar a sallami duk wasu ‘yan siyasa da ake tsare da a kasar.
Matakin dai na zuwa yini guda bayan sallamar dan adawa Ousmane Sonko .
Bayan sallamar shi Ousmane Sonko, ya bukaci da zazafa zanga zanga amma cikin lumana.
Saidai a wani jawabi da ya yi irinsa na farko tun bayan barkewar zanga zangar, shugaban kasar Macky Sall, ya bukaci a kai zuciye nesa.
Haka kuma, shugaban ya yi alla-wadai da rikicin inda a kalla mutum biyar suka mutu sannan ya yi kira ga ƴan kasar su kwantar da hankulansu.
Tun farko gamayyar jam’iyyun adawa a Senegal sun bukaci al’ummar kasar da su mara musu baya wajen gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin daga ranar Litinin har tsawon kwanaki 3.
342/