9 Maris 2021 - 12:11
Iran:Wata Ba’iraniya Gurguwa Ta Sami Kyauta A Ranar Mata Ta Duniya

Kwamitin wasannin paraolimpic ta kasa da kasa ta bada sanarwan cewa ta bawa bawa Zahra Nimati wata gurguwa ‘yar wasan motsa jiki tana daga cikin wadanda suka sami kyautar. Kamfanin dillancin labaran IRNA y ace Zahra it ace ta fara samun lambar yabo ta azurfa a gasannin paraolympic ta duniya.

ABNA24 : Labarin ya kara da cewa mata uku ne kwamitin paraolimpic ya za ba don samun wannan kyautar. Zahra Nimati dai ‘yar wasan motsa jiki ne a nan kasar Iran wacce ta sha halattar wasannin kasa da kasa na guragu.

Labarin ya kara da cewa Zahra Nimati ta sami lambar yabo ta zinari a wasannin paraolimpic wadanda aka gudanar a shekara ta 2012 a birnin London na kasar ingila. Har’ila yau ta taba halattar taron kasa da kasa ta guragu wanda MDD ta shirya.

342/