ABNA24 : Shuaib ya kara da cewa an kammala dukkan shirye shirye a duk fadin kasar don ganin an fara amfani da alluran a dukkan jihohin kasar bisa tsarin da gwamnati ta bayar.
Da farko dai za’a fara yiwa jami’an kiwon lafiya ne da kuma wadanda suke aiki tare da su sannan tsoffin mutane da sauransu.
A ranar jumma’an da ta gabata ce aka fara yin alluran riga kafin cutar Korona a tarayyar Najeriya inda shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osingbajo suka fara karban alluran a bainal jama’a.
342/