ABNA24 : Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta Equatorial Guinea ce ta sanar da adadin mutanen da su ka rasu sandiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfin gaske har sau 4 a wani barikin soja dake garin Bata a jiya Lahadi.
Su ma Kafafen watsa labaru kasar ta Equatorial Guinea sun bayyana cewa; Adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 20, yayin da wadanda su ka jikkata suka haura 500.
Shugaban kasar ta Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguemawanda ya gabatar da jawabi ga al’ummar kasar ta kafafenw watsa labaru ya bayyana cewa sakaci da rashin kula shi ne ya haddasa fashewar nakiyoyi da bama-bamai a a cikin barikin na soja.
342/