2 Maris 2021 - 11:16
​Araqchi: Fitar Da Kudirin Suka Kan Iran A Zaman IAEA Zai Kara Dagula Lamurra Tsakanin Iran Da Hukumar

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, yunkurin da kasashen turai suke yi na ganin an fitar da kudirin sukar kasar Iran a zaman alkalan hukumar IAEA, yin hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

ABNA24 : A wata zantawa da ta gudana a daren jiya tsakanin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi, da kuma babban wakilin ma’aikatar kula da harkokin tarayyar turai a kasar Austria Peter Lavonsky, Araqchi ya bukaci kasashen turai da su sake yin nazari kan matakan da suke dauka dangane da Iran, kan batun shirinta na nukiliya.

Ya ce daukar matakin yin suka ga kasar Iran a babban taron hukumar makamashin nukiliya ta duniya, babu abin da zai haifar illa kara sanya tazara da kara nisanta hukumar da kuma Iran, wanda kuma kowa ya san hakan ba maslaha ce ga hukumar ba, da ma su kansu kasashen turai.

Ya ci gaba da cewa, Iran tana nan kan bakanta, kuma abin da ta fada bai saba wa wata doka ba, idan an janye mata takunkumai za ta koma yin aiki da dukkanin bangarorin yarjejeniyar nukiliya da ta jingine yin aiki da su.

Shi ma a nasa bangaren babban wakilin ma’aikatar kula da harkokin tarayyar turai a kasar Austria Peter Lavonsky, ya sheda wa Araqchi cewa, kasarsa tana goyon bayan ganin an yi amfani da hanyoyi na diflomasiyya wajen warware wannan matsala, tare da jaddada cewa kasarsa tana da tsohuwar alaka da kasar Iran, kuma babu abin da zai yi tasiri a kan wannan alaka.

342/