2 Maris 2021 - 11:10
​ Nijar : An Tisa Keyar Hama Amadou Zuwa Kurkuku

A jamhuriyar Nijar, an tisa keyar madugun ‘yan adawa na kasar Mal. Amadou, zuwa gidan yarin Filingue, kwanaki uku bayan tsarewar da aka mishi.

ABNA24 : A ranar Juma’a data gabata ne Hama Amadoun ya mika kansa ga hukumar ‘yan sandan farin kaya ta (PJ), a Yamai, bayan da hukumomin kasar suka zarge shi da hannu a ingiza rikicin da ya biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

Hukumomin kasar na dai zargin Hama Amadou da gomman laifuka da suka hada da farfaganda ta nuna kabilanci, da tunzura masu zanga zanga lalata dukiyoyin jama’a da kuma tarzomar da aka kwashe kwanaki anayi a kasar bayan sanar da sakamakon zaben da hukumar kasar ta CENI, ta sanar cewa dan takarar jam’iyya mai mulki ne lashe.

Lauyen Hama Amadou, Boubacar Mossi ya kalubanlanci matakin da cewa shari’a ce ta nuna karfin iko, saboda wanda yake karewa bai yi wani firici ba game sakamakon zaben da aka sanar a ranar Talata data gabata.

Baya ga Hama Amadoun, da akwai wasu ‘yan siyasa da dama da aka cafke, sai kuma Janar mai ritaya Moumouni Boureima wanda aka tisa keyarsa a gidan kason Ouallam.

342/