27 Faburairu 2021 - 08:43
​Zamfara: An Bayar Da Umarnin Rufe Dukkanin Makarantun Kwana

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana da suke a cikin jihar, biyo bayan yin garkuwa da daliban makarantar Sakandaren mata dake Jangebe, da ke cikin karamar hukumar Talatar Mafara.

ABNA24 : Rahotanni sun ce maharan sun sace dalibai mata fiye da 300 a daren Juma’ar da ta gabata, inda gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya bayyana cewa tuni gwamnati ta aike da jami’an tsaro domin ceto wadannan ‘yan makaranta da aka sace.

Gwamnan ya bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana da suke cikin jihar har sai abin da hali ya yi sakamakon abin da ya faru.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a kan makarantar sakandaren ta mata da ke Jangebe ne a tsakar daren Alhamis, inda suka kewaye makarantar, kuma suka ci gaba da yin harbe-harbe da bindigogi na tsawon fiye da awa daya, daga nan kuma suka yi awon gaba da ‘yaran da suka tattara, wadanda yawansu ya haura 300.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa tana ci gaba da bin kadun lamarin domin tabbatar da cewa an ceto wadannan yara daga hannun ‘yan bindigar, kamar yadda kuma gwamnan jihar ya kirayi mutane da su rika bayar da hadin kai, wanda zai taimaka wajen ganin an samu nasarar yin hakan.

Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta yi imanin cewa hanyar tattaunawa tare da ‘yan bindiga domin su ajiye makamansu su daina harkar ta’addanci ita ce hanya mafi dacewa domin kawo karshen wannan matsala, tare da daukar matakai na soji a kan wadanda suka ki amincewa da sulhu.

342/