12 Faburairu 2021 - 13:55
​Lavrov: Rasha A Shirye Take Ta Yanke Alaka Da Tarayyar Turai

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov ya bayyana cewa, Rasha a shirye take ta yanke alaka da kungiyar tarayyar turai, matukar kungiyar ta kakaba wa Rasha wasu sabbin takunmai da za su cutar da tattalin arzikinta.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov a zantawarsa da wata kafar yada labarai a yau Juma’a, ya bayyana cewa, Rasha a shirye take ta yanke dukkanin alakokinta da kungiyar tarayyar turai, matukar kungiyar ta saka wa Rasha wasu sabbin takunmai a bangarorin da za su cutar da tattalin arzikin kasar ta Rasha.

Ya ce Rasha a shirye take domin daukar kowane irin mataki da ya dace domin fuskantar barazanar kungiyar tarayyar turai ta baya-bayan nan, inda take tunanin kakaba wa Rasha takunkumi domin cutar da tattalin arzikinta.

Tarayyar turai ta bayyana cewa za ta dauki wannan matakin ne sakamakon yanke hukuncin daurin shekaru biyu da kimanin watanni 10 da aka yi wa dan adawa Alexei Navalny akasar Rasha, bisa zarginsa da karya dokar daurin talala, a kan zargin da ake yi masa na halasta kudaden haram, da kuma korar wasu jami’an diflomasiyyar turai da Rasha ta yi, bayan da suka shiga cikin zanga-zanga a kasar ta Rasha ta magoya bayan Navalny.

342/