ABNA24 : Shugabannin kasashen Afrika sun sake zabarsa a lokacin taron kolin kungiyar karo na 34, wanda aka bude a jiya Asabar ta kafar bidiyo.
A cewar AU, mambobi 51 daga cikin 55 ne suka zabi Mahamat.
Dama dai Musa faki Mahamat, shi ne dan takara daya tilo da ya tsaya a zaben neman shugabancin kungiyar.
A ranar Asabar ne shugaban gudanarwar kungiyar ta AU ya gabatar da bayanan muhimman ayyukan da ya gudanar a wa’adin shugabancinsa na farko ga taron majalisar shugabannin kasashen Afrika.
342/