ABNA24 : Za’a kwashe mako guda bangarorin na tattaunawa domin zabar sabon firaminista da kuma mambobin majalisar zartaswa da zata yi rikon kwarya kafin zabubukan kasar a watan Disamba.
Saidai a baya baya nan ana nuna shakku game da batun samar da zaman lafiya a kasar a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a birnin Tripoli, duba da rikicin da ya kunno kai tsakanin firaministan kasar mai murabus, Fayez el-Sarraj, da ministan cikin gida na kasar Fathi Bachagha, wanda ake ganin zai iya zama sabon firaministan kasar.
Tuni dai kungiyar ICG, dake sanya ido kan rikice rikice a duniya, ta yi gargadi game da rashin samun fahimtar juna tsakanin bangarorin ‘yan siyasar na Libiya, a wannan tattaunawar, wanda a cewar kwararun kungiyar dukkan bangarorin na da karfin siyasa, soji da kuma kudi, domin wargaza tattaunawar ta Geneva ta hanyar kin amincewa da zaben ko sakamakonsa.
342/