ABNA24 : Ofishin shugaban kasar ya ayyana kafa dokar ta bacin bayan sojojin kasar sun kifar da gwamnati tare da tsare shugabar gwamnatin kasar, Aung San Suu Kyi, da shugaban kasar U Win Myint, gami da wasu manyan kusoshin gwamnatin kasar.
Sojojin sun bayyana cewa a cikin wa’adin dokar ta bacin da aka kafa, za a kafa hukumar da zata jagoranci shirya zaben kasar kuma za a yi sauye sauye a zaben majalisar dokokin kasar wanda aka gudanar a watan Nuwambar bara.
A sanarwar da aka fitar ta gidan talabijin din kasar na Myawaddy TV wanda sojojin suka karbe ikonsa, ance za a mika ragamar shugabancin kasar ga babban hafsan tsaro na kasar Myanmar, Min Aung Hlaing.
342/