ABNA24 : Kamfanin dillancin rabaran IRNA na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi yana fadar haka a jiya Talata a kasar Kuwait a lokacinda yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar ta Kuwait Sheikh Ahmad Nasir Almuhammad Assabah.
Labarin ya kara da cewa Araqchi ya yabawa kasar ta Kuwait wacce ta shiga tsakanin don sasanta kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa a tsakaninsu.
Anashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Kuwai ya yabawa Jumhuriyar Musulunci ta Iran kan kokarin da take yi na tattaunawa da kasashen yankin saboda tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin.
342/