ABNA24 : Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran a safiyar yau Asabar, kan cewa Iran kanta ta sha gamuwa da ayyukan ta’addanci na kungiyoyin ‘yan ta’adda daga cikin har da kungiyar Al-Qaeda, sannan ita ce a kan gaba wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda a duniya.
Zakharova ta kara da cewa kasar Iran ta taka rawan a zo a gani wajen yakar kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasashen Iraki da Siriya.
A ranar tarlatan da ta gabata ne sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi kasar Iran da zama sabuwar matattaran kungiyar Al-Qaeda, a waton taron ‘yan jarida da ya yayi.
A maida martani ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zareef ya bayyana cewa, a dai-dai sauran ‘yan kwanaki ikon gwamnatin Trump ta kare, Pompeo yana fushi da gazawar gwamnatinsu wajen durkusar da gwamnatin Iran ta hanyar takunkuman tattalin arziki mafi muni a kan kasar.
342/