ABNA24 : Babban kwamandan dakarun IRGC a bangaren tsaron sararin samaniyya Brigadier General Ali Hajizadeh ya bayyana cewa, a wannan atisayin an gwada sabbin makamai masu linzami wadanda Iran ta kera, wadanda ake sarrafa su daga tazara mai nisa da na’urori na zamani.
Ya ce babban aiki wadannan makaman shi ne ragargaza tsarin kariya ta sama na rundunar makiya, ta yadda makaman za su iya ta tarwatsa makaman kariya na makiya da suke girke a doron kasa, ko kuma bayan harba su a cikin sararin samaniya.
Baya ga haka kauma ya kara da cewa, an gwada wasu sabbin jiragen yaki marasa matuki masu tsananin sauri da Iran din ta kera, wadanda za su iya kai hari daga tazara mai nisa, a lokaci guda kuma suna kauce wa na’urar radar ta makiya ba za ta iya gane su a cikin sararin samaniya ba.
Ya ce duk wannan yana zuwa ne domin kara zama cikin shirin ko ta kwana domin fuskantar kowace irin barazana daga makiya, tare da tabbatar wa masu tunanin cewa za su iya taba kasar su kwana lafiya da cewa, hakan ba a bu ne mai sauki ba.
342/