ABNA24 : Wannan bayanin ya fito daga bakin shugaban kwamitin yaki da annobar Korona ta gwamnatin tarayya (PTF) Boss Mustapha yayin wata zantawa da ‘yan jarida a Abuja.
Boss Mustapha ya kara da cewa an wallafa jerin sunaye 100 na ‘yan Nijeriyan da suka ki yin gwajin cutar Korona na biyu da aka dakatar da iznin fitarsu na tsawon wata shida.
Ya ce dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2021, “A karon farko an dakatar da Fasfo din fasinjoji ‘yan Nijeriya 100 wadanda suka ki bin matakin gwajin cutar Korona na bayan kwana bakwai da dawowarsu, za mu wallafa sunayen wadanda lamarin ya shafa a manyan jaridun Najeriya,” inji shi.
Ya ce: kasarmu tana fuskantar kalubalen yiwuwar barkewar korona zango na biyu. Dole ne mu kara daukar matakan kariya da kiyaye yaduwar cutar, domin a cikin makonni 52 zuwa yanzu, ana samun yawaitar masu kamuwa da cutar corona a Najeriya, inda bincike ya nuna cewa, kashi 16 cikin 100 na wadanda aka yi musu gwaji sun kamu da cutar.
342/