20 Disamba 2020 - 11:53
Sudan : Ana Kukan Rashin Sauyi, Shekaru Biyu Bayan Kifar Da Al-Bachir

A Sudan dubban ‘yan kasar ne suka gudanar da wata zanga zanga, kan rashin ganin sauyi a yayin da aka cika shekara biyu da boren da ya kai ga kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Umar Hassan Al’bachir.

ABNA24 : Masu zanga zangar da suka nufi fadar shugaban kasar a Khartoum, na masu raira taken neman shari’a, da kuma neman kawo karshen mulkin da kasar ke kansa a yanzu.

A ranar 19 ga watan Disamba na shekara 2018 ne, daruruwan ‘yan Sudan suka fara zanga zanga a wasu biranen kasar, bayan matakin waccen gwamnati na linka kudin berdi har sau uku a daidai lokacin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki, lamarin da ya rikide zuwa ga boren da ya kai ga sojoji suka hambarar da mulkin Umar Al-Bashir a ranar 11 ga watan Afrilun shekarar 2019, bayan ya shafe shekaru 30 yana jan ragamar shugabancin kasar.

Bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin sojojin da kuma jagororin masu zanga zanga a yanzu kasar na karkashin gwamnatin wucin gadi, da firaminista Abdallah Hamdok ke jagoranta, saidai kawo yanzu ‘yan kasar na cewa babu wani sauyi da suka gani a zahiri, sannan har yanzu ba’a gurfanar da wadanda suka murkushe masu zanga zanga ba.

Ko bayan matakin baya bayan nan da Amurka ta dauka na janye kasar ta Sudan daga jerin kasashe masu goyan ta’addanci, babu wani canji da aka soma fuskanta musamman a wani lokaci da kasarke fama da annobar korona da kuma hauhawan farashin kayayaki.

342/