ABNA24 : Mutane miliyan 20, da dubu 700 ne ke kada kuri’a a zaben, wanda yan adawa dake rike da majalisar tun cikin 2015 suka bukaci jama’a dasu kauracewa zaben.
A nasa bangare shugaban kasar Nicolas Maduro, ya bukaci jama’a dasu fito dafifi domin kada kuri’arsu, idan suka bukatar a farfado da tatalin arzikin kasar.
Tattalin arzikin Venezuela dai ya fuskanci mummunan koma baya sakamakon jerin takunkuman Amurka.
342/