1 Disamba 2020 - 10:44
An Sami Tashin Gobara A Cikin Manyan Rijiyoyin Man Fetur A Hadaddiytar Daular Larabawa

An Sami Tashin Gobara A Cikin Manyan Rijiyoyin Man Fetur A Hadaddiytar Daular Larabawa

ABNA24 : Kafafen watsa labarun kasar ta HDL sun ambaci cewa; gobara ta tashi a cikin rijiyoyin man fetur na “Zakum’ da ke Abu Dhabi, da kuma wasu rijiyoyin na “Al-Fatih”.

Kafar watsa labaru ta “ Bulletine News” ta ambaci cewa; An ji karar fashewar wasu abubuwa sannan kuma da tashin gobara a cikin rukunin manyan rijiyoyin biyu na Zakum a Abu Dhabi da kuma naal-Fatih a Dubai.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani akan abinda ya haddasa gobarar a cikin rijiyoyin na man fetur da ake dauke na biyu mafi girma a duniya.

342/