23 Nuwamba 2020 - 17:45
Firayi Ministan Habasha Ya Sake Ba Wa ‘Yan Awaren Tigray Wa’adin Kwanaki 3 Su Mika Kai Ko Su Fuskanci Fushin Gwamnati

Firayi ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya ba wa ‘yan awaren yankin Tigray na kasar wa’adin kwanaki uku na su mika kai ko kuma gwamnatin ta kaddamar da wasu sabbin hare-hare kan babban birnin yankin, Mekelle.

ABNA24 : Firayi minista Abiy ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce: Muna kiranku da ku mika kai cikin ruwan sanyi cikin sa’oi 72, don kuwa a halin yanzu an kai matakin da babu ja da baya.

Yayin da ya ke magana kan wannan wa’adin, kakakin sojin kasar Habashan Dejene Tsegave ya kirayi fararen hula da suke birnin na Mekelle da su raba gari da mahukuntan yankin, yana mai bayyana musu cewa idan lamarin ya kai ga hare-hare to fa ba sani ba sabo in ji shi.

A na su bangaren shugaban jam’iyyar Tigray People's Liberation Front (TPLF) Debretsion Gebremichael mai mulki a yankin ya sha alwashin cewa dakarunsu za su yi tsayin daka da kuma tinkarar sojojin gwamnatin da dukkan karfinsu don kare babban birnin yankin; yana mai cewa lalle sojojin gwamnatin za su fuskanci turjiya mai tsananin gaske matukar suka dunfaro garin.

A wata sabuwa kuma MDD ta kirayi gwamnatin Habashan da ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen kare rayukan fararen hula da yakin ya ritsa da su wadanda aka ce fararen hulan da suke garin na Mekelle sun kai 525,000.

342/