22 Nuwamba 2020 - 13:23
Mutane 5 Sun Mutu A Yayin Da ‘Yan Sanda Ke Ci Gaba Da Neman Fursunonin Da Suka Gudu A Kasar Labanon

Jami’an tsaro a kasar Labanon sun kaddamar da wani shirin farautar kimanin fursunoni 70 da suka gudu daga wani gidan yari a kasar bayan fasa dakunan kwanansu da kuma kai hari kan jami’an tsaron gidan yarin da suka yi a daidai lokacin da wasu biyar daga cikin fursunonin da suka gudun suka mutu.

ABNA24 : Rahotanni daga kasar sun ce wannan lamari na balle gidan yarin da kuma gudun fursunonin ya faru ne a jiya Asabar a bangaren da ake tsare da fursunonin da ake musu shari’a na gidan yarin Baabda da ke babban birnin kasar, Beirut.

A wata sanarwa da ‘yan sandan kasar suka fitar, sun ce biyar daga cikin fursunonin da suka gudun sun mutu a lokacin da motar da suka sata a yayin da suke gudun ta yi hatsari biyo bayan bibiyansu da ‘yan sandan suke yi.

Har ila yau ‘yan sandan sun ce jami’an tsaron sun sami nasarar sake kama 15 daga cikin fursunonin da suka gudun sannan wasu 4 kuma daga cikin wadanda suka gudun sun mika kansu ga jami’an tsaron, a daidai lokacin da jami’an tsaron suka yi wa yankin kawanya a ci gaba da kokarin kame furusnonin da suka gudun.

Mahukunta a kasar Labanon din dai sun ce tuni shugaban kasar ya ba da umurnin a gudanar da bincike kan wannan lamarin da ya faru wanda wasu suke ganin kamar akwai hadin baki tsakanin fursunonin da wasu daga cikin masu gadin gidan yarin da hakan ya ba su damar gudu daga inda ake tsare da su din.

342/